Yadda Ake Dambun Kaza - Arewaweb

Yadda Ake Dambun Kaza

< ;

danbun-kaji.jpg


Idan kika gyara kajinki tas! Saikicire
masa fatar dake jiki gaba daya
kiwanke yadda ya kamata Saiki zuba
a tukunya amma kizuba ruwa kwatan
kwacin yadda naman zai shanye,

karki zuba dayawa, kidora kiyanka
albasa, maggi, gishiri, curry, da kayan
qamshi zabinki, saiki rufe kibarta tayi
tafasa dakin bude kinga naman yayi
laushi zaki sauke qasa saiki sa
muciya kiyi ta faffasa naman


idan aki cire fatar yana danye ba to
yanzu saiki zare duk fatar da manyan
qashi kiyta faffasawa zakiga naman
yafito sanka-sanka saiki jajjaga
taruhunki sosai, kijuye akai ki qara
curry da kayan qamshin dakike so, ki
gauraye ya hade nam an, saiki samu
abun suya mai dan dama kizuba mai
dayawa

cux inkika masa qwauron mai
kwata kwata bazaiyi kyau ba, sannan
bazai laushi ba,saiki dauko namanki
kijuye aciki kidora awuta kipara
soyawa sannan kisa wuta kadan
ahankali kina juyawa akai akai,idan
ya soyu zakiga yayi ja sannan mai
zaipara kumpa kuma zakiji qamshi
saiki sauqe kijuye a colander ya huce
saiki dan saka plate asama kimatse
mai duk zai fito, shikenan!

No comments

Powered by Blogger.