YADDA ZAKA NEMI AIKIN N,POWER CIKIN SAUKI 5 November 2018 - Arewaweb

YADDA ZAKA NEMI AIKIN N,POWER CIKIN SAUKI 5 November 2018

< ;
  1. 1.Mafi karancin kwalin da ake bukata a wannan bangaren shi ne kwalin sakandire (SSCE result).
  2. 2. Asusun Banki (Bank Account)
  3. 3. BVN Ka tabbata sunan da zaka yi amfani da shi ya yi daidai da wanda yake cikin BVN dinka, haka zalika shekarun haihuwa.
  4. 4. Kanann Hotuna (Passpot)
  5. 5. ID card ( Voters' card ko National Id card)
  6. 6. Za a shiga www.npower.gov.ng domin cike takardar neman wannan aikin (Application Form)
  7. Kamar yadda sanarwa ta gabata makon da ya gabata cewa gwamnatin tarayya zata dauki sababbin ma'ikata na Npower, to a wannan karan za a koyar da sana'o'i ne wanda suka hada da;
  8. 1. AUTOMOBILE: Wannan bangaren ya shafi koyar da hanyoyin gyaran mota na zamani ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa wanda ya hada; OBD scanner da wheel balancing da kuma panel beating.
  9. 2. Agriculture Equipment Technicians (Agric Tech) : Shi kuma ya shafi yadda za a sarrafa Motoci da injuna da ake amfani da su wurin noma, da kuma yadda ake kula da su.
  10. 3. CARPENTRY & JOINERY : A nan kuma za a koyar da aikin kafinta, musamman na bangaren aikin gini, ma'ana kafintan Sama.
  11. 4. ELECTRICAL INSTALLATION: wannan bangaren kuma yana kunshe da fannin wayarin na wuta da kuma gyaran wuta.
  12. 5. MASONRY & TILING : Shi kuma wannan za a koyar da aikin gini ne da kuma yadda ake saka tayil da falasta da kuma dabe.
  13. 6. PLUMBING & PIPEFITTING : A wannan bangaren kuma za a koyar da abin da ya shafi yadda ake yin wayarin din ruwa da kuma yaddaa ake hada hitar wanka ta zamani da yadda ake shirya fayif -fayif na ruwa.
  14. 7. HOSPITALITY: Shi kuma wannan aji ya kunshi yadda ake hada kayan kwalam da makulashe kamar su kyak(cake) da kuma gike-girke na zamani. Wannan kusan shi ne yake da alaka da mata kai tsaye.
kadda kayi rowar yin share din wannan abun koda ko bakaso akwai masu so,
yadda zakai share shine kabi links din share da muke dashi anan kayi share dinshi akwai lada sosai idan ya zama cewa mutane 
sun samu a dalilin share dinka allah ya bada sa.a amin summa amin

3 comments:

Powered by Blogger.