An gano wata hanya da HIV ke kara yaduwa a tsakanin ‘yan Najeriya - Arewaweb

An gano wata hanya da HIV ke kara yaduwa a tsakanin ‘yan Najeriya

< ;


- Hukumar kula da kuma shawo kan yaduwar ciwon kanjamau a jihar Nasarawa ta bayyana cewar fara jima’I a kananun shekaru na daga cikin abubuwan dake kara yada cutar kanjamau

- Dakta Ruth Adabe, darekta a hukumar, ce ta sanar da haka a yau, Alhamis, a Keffi yayin wani taro a kan hanyoyin yaduwar cutar kanajamau
- Kungiyar kula tare da kare hakkin yara (UNICEF) tare da hukumar wayar da kan jama’a ta (NOA) ne suka shirya taron

Hukumar kula tare da dakile yaduwar cutar kanjamau ta jihar Nasarawa ta bayyana cewar fara jima’i a kananun shekaru na daga cikin abububwan dake assasa yaduwar cutar kanjamau a tsakanin ‘yan Najeriya.

Darekta a hukumar, Dakta Ruth Adabe, ta sanar da hakan a yau, Alhamis, yayin gabatar da jawabi ga manema labarai da ‘yan jarida a kan abubuwan dake assasa kamuwa da ciwon kanjamau tsakanin ‘yan Najeria a wani taro da kungiyar kula tare da hakkin yara (UNICEF) da hadin gwuiwar hukumar wayar da kai ‘yan kasa (NOA) suka shirya a Keffi, jihar Nasarawa.
An gano wata hanya da kanjamau ke kara yaduwa a tsakanin ‘yan Najeriya

Dakta Adabe, wacce Dakta Peter Attah, shugaban sashen dakile yaduwar cutar kanjamau, ya wakilta, ta bayyana cewar yiwa kananan yara aure da kuma rashin bawa matasa ilimin jima’i na daga cikin sahun matsalolin dake saka cutar kara yaduwa a tsakanin ‘yan Najeriya.


Dakta Adabe ta sanar da cewar yanzu cutar kanjamau na kara yawa a tsakanin matasa saboda fara jima’i a kananun shekaru, lokacin da sha’awa ke da karfi a jikinsu kuma ba tare da sun samu ilimin jima’i ba.

No comments

Powered by Blogger.