Wane ne Sheikh Muhammad Hassan? Rubutawa Sheikh Dr Mansur Sokoto. - Arewaweb

Wane ne Sheikh Muhammad Hassan? Rubutawa Sheikh Dr Mansur Sokoto.

< ;


Yaumut Tarwiyah, 1439H (18/08/2018)
Sunansa: Sheikh Muhammad Hassan Bn Ibrahim Al-Mansuriy Al-Misriy Al-Salafy:

- Dattijo ne dan shekaru kusan 60
- Ya hardace Alkur'ani yana dan shekaru 8 tun sama da shekaru 50 kenan. Ga shi da zakin murya da iya rera Alkur'ani. Ma sha Allah!

- Ya hardace Littafai masu tarin yawa na Aqida da Fiqihu da Hadisi da fannonin larabci tun yana yaro karami.
- Yana limancin Sallar tarawihi tun sama da shekaru 40
- Yana limancin sallar Jum'ah tun yana dan shekaru 13, sama da shekaru 45 kuma har yanzu yana akai.
- Sama da mutane dubu 30 suke halartar hudubarsa a wasu lokutan.

- Shi ne chairman na Majma' Ahlis Sunnah a kasar Masar
- Tare da tarin iliminsa, mutum ne mai natsuwa da tawali'u da saukin kai matuka. Ni shaida ne don ko a jiya da muka hadu na ga haka.

- A lokacin da yake matashi ya mayar da hankali ne sosai a cikin hudubobinsa da wa'azojinsa a kan Kiristanci da Yahudanci da yadda suka gurbata addininsu. Sai ya kasance a kullum kiristoci musulunta suke yi a hannunsa. Manyan kiristocin kasar Masar suka taso shi a gaba, hukumomi suka shiga cikin maganar, tsangwama ta yi masa yawa, abinda ya sa dole ya yi hijira ya koma kasar Saudia.

- A nan ne fa ya samu ya yi karatu a hannun wadannan Manyan Malamai na kasar Saudia:

1. Sheikh Abdulaziz Bn Baz
2. Sheikh Muhammad Bn Saleh Al-Uthaimin
3. Sheikh Abdallah Bn Jibreen
4. Sheikh Abdulkadir Shaibat Al-hamd

- Ya tafi wurin Sheikh Bn Baz ne tare da malaminsa Sheikh Safwat Nuruddin, inda suka sauke Manyan littafai da dama a hannun Bn Baz, cikin su har da Fathul Bari da Sharhin Nuniyyah ta Ibnul Qayyim, da Sharhin Wasitiyyah da na Dahawiyyah da littafan Fiqhu da Usulul Fiqhi da dama.

- A lokacin da yake digirinsa na farko ya yi tafiyayya a lokacin wani dogon Hutu zuwa Jordan wurin Sheikh Muhd Nasiruddin Al-Albani ya kwashi karatu Mai yawa. A dan wannan lokacin kuma sai da aka sa shi limancin wani Masallacin jum'ah a can Jordan.

- Ya sauke Tafsirin Alkur'ani a wurin Sheikh Abdallah Bn Jibreen da wasu littafan Aqida da Fiqhu da Usulul Fiqh.
- A wurin Sheikh Abdulkadir Shaibat Al-hamd ya karanci sharhin Bulugul Maram.

- Ya dauki dogon lokaci a birnin Qaseem wurin Sheikh Saleh Al-Uthaimin inda ya kwashi karatu Mai yawa Mai albarka. Saboda amincewa da shi Sheikh Uthaimin ya sa shi karantarwa a Kolejin Shari'a da Kuma Kolejin Usuluddin Na jami'ar Muhammad Bn Su'ud da ke Qaseem, in da ya koyar da Hadisi da kimiyyarsa da ilimin sanin maruwaita da hanyoyin fitar da Hadisi da sauransu.

- Bayan ya yi shekaru yana koyarwa a wannan jami'ar ne Sheikh Sulaiman Ar-Rajihi ya nemi ya dawo masallacinsa na Qaseem in da ya ci gaba da ba da Sallar jum'ah tare da shaihun Malamin.

- Akwai Wani lokaci da Manyan Malamai na kasa suka halarci wannan Masallaci, sheikh Sulaiman ya sa Muhammad Hassan ya yi Huduba Kuma ya ba da Sallah. Bayan sallama Sallar ne Malaman suka gana da junansu kuma suka amince da ba shi digirin girmamawa na PhD wanda Sheikh Abdallah Bn Mani' ya tashi ya sanar a gaban jama'a a madadin su Sheikh Bn Baz da Uthaimin da sauran Manyan Malamai na kasa.

- Ya fara yin digirinsa na farko ne a Cairo University, sannan ya rubuta PhD thesis dinsa a jami'ar Amerika da ke Cairo inda Manyan Shaihunan Azhar suka duba shi kuma suka ba shi martaba ta kolin tare da girmamawa. Ya yi rubutu ne a kan "Tafarkin Annabi (S) wajen kiran wadanda ba Musulmi ba".

- Ya taba yin Huduba a kan Yahudawa da makircinsu, wadda a cikin ta ya ambaci sunan Kamal Ataturk (tsohon shugaban kasar Turkiyya) da yadda Yahudawa suka yi amfani da shi don rusa Daular Musulunci. Allah ya sa ma wannan Hudubar karbuwa sosai duk ta game kasar Masar. A rubuce, ofishin Jakadancin kasar Turkiyya ya aike ma Ministan harkokin wajen kasar Masar (Amru Musa) suna karar Sheikh Muhammad Hassan a kan wannan Huduba.

Da Ministan ya saurari Hudubar sai ya ce, ai wannan wajibi ne a yada ta duk duniya a ji ta. Amma ya sa aka cire sunan Kamal Ataturk saboda gyara alakarsu da kasar ta Turkey.

- A New York ta Amerika ya taba yin wa'azi mutane 75 suka musulunta kai tsaye.
- Ya yi limancin sojoji a lokacin da ya yi hidimar kasa bayan gama jami'a.

- Allah ya ba shi kaifin basira da hazaqa da fasahar magana ta kin karawa. Ga saurin iya kafa hujja da nassoshin Shari'a. Ba ya kafa hujja da Hadisi sai ya fadi asalinsa kuma ya tabbatar da ingancinsa.

- Allah ya ba shi karbuwa a tsakanin Ahlus Sunnah na ko Ina a duniya. Duk inda ya je al'umma na Marhaba da shi, tare da so da kauna da darajantawa.
- Kasusuwansa na hudubobi da darussa da wa'azoji akan tafarkin Sunnah sun game duniya tun kafin zamanin intanet.

- Idan zai yi limancin Sallar jum'ah a Masjidut Tauhid ko Masjidur Rahmah ko sauran fitattun masallatan Ansarus Sunnah (Izalar Misra) duk titunan da suke isa zuwa wurin sai sun cika sun batse.

- An san shi da matsakaicin ra'ayi; ba ya shiga husuma ko jayayya, ba shi kuma son fitina da tashin hankali da raba kan jama'a.

- Ya wallafa Littafai masu yawa sosai. Ya kuma gabatar da daruruwan kasidu a taruka daban daban a kasashen duniya, ban da hudubobi na Sallar jum'ah wadanda su ma ya gabatar a kasashen Musulmi da yawa da na turawa. Daga cikin littafansa akwai:

١ . ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ
٢ . ﺧﻮﺍﻃﺮ ﻋﻠﻰ ﻃﺮﻳﻖ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ
٣ . ﻗﻮﺍﻋﺪ ﺍﻟﻤﺠﺘﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ
٤ . ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺑﺎﻟﻘﻀﺎﺀ ﻭﺍﻟﻘﺪﺭ
٥ . ﺍﻟﺜﺒﺎﺕ ﺣﺘﻰ ﺍﻟﻤﻤﺎﺕ
٦ . ﺃﺋﻤﺔ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﻣﺼﺎﺑﻴﺢ ﺍﻟﺪﺟﻰ
٧ . ﺟِﺒْﺮِﻳﻞ ﻳﺸﺄﻝ ﻭﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺠﻴﺐ ‏( ٣ ﻣﺠﻠﺪﺍﺕ ‏)
٨ . ﻣﺴﺎﺋﻞ ﻣﻬﻤﺔ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﻨﻬﺠﻴﺔ ﻭﺍﻟﺤﺮﻛﻴﺔ
٩ . ﺃﺣﺪﺍﺙ ﺍﻟﻨﻬﺎﻳﺔ ﻭﻧﻬﺎﻳﺔ ﺍﻟﻌﺎﻟﻢ
١٠ . ﺩﺭﻭﺱ ﻣﻦ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻨﻮﺭ
١١ . ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻤﻨﺎﻓﻘﻴﻦ
١٢ . ﺩﺭﻭﺱ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﺮﺑﻴﺔ
١٣ . ﻗﺒﺲ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻨﺔ
١٤ . ﺣﻘﻮﻕ ﻳﺠﺐ ﺃﻥ ﺗﻌﺮﻑ ‏( ٣ ﻣﺠﻠﺪﺍﺕ ‏)
١٥ . ﺍﻟﺴﻴﺮﺓ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺤﺎﺿﺮ ﻭﺍﻟﻤﺎﺿﻲ


 Ya gabatar da dubunnan darussa ta kafafen sadarwa (Radiyo da Talabijin) kamar wadannan shiraruwa:

- ﺇﻧَّﺎ ﻋﺎﻣﻠﻮﻥ
- ﺃﺯﻣﺔ ﺃﺧﻼﻕ
- ﻛﻠﻤﺔ
- ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﺮﺣﻤﺔ
- ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ
- ﻣﻦ ﺑﻴﻮﺕ ﺍﻟﻠﻪ
- ﺃﺋﻤﺔ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﻣﺼﺎﺑﻴﺢ ﺍﻟﺪﺟﻰ
- ﺍﻟﻘﻀﻴﺔ
- ﺃﻣﺮﺍﺽ ﺍﻷﻣﺔ
- ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﺮﺣﻤﺔ
- ﺟِﺒْﺮِﻳﻞ ﻳﺴﺄﻝ ﻭﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺠﻴﺐ ‏( ﻓﺘﺎﻭﻯ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻘﻴﺪﺓ )

- Ana iya samun da yawa daga cikin karatuttuka da hudubobinsa a wadannan kafaifan:

www.islamway.com
www.saaid.net
www.al-eman.com
www.shabkh.com

Bayan haka,
Wannan shi ne tarihin wannan bawan Allah wanda muka ci karo da shi a birnin Manzon Allah (S) a jiya. Kamar yadda muka gani, duk tsawon rayuwarsa bai san wani abu ba ban da karatu da karantarwa, da shiryar da mutane zuwa ga Sunnar Manzon Allah (S).

Idan kuka ji wasu shaidanu, kananan yara, marasa kunya da tsoron Allah, sun sha gubar cin mutuncin Malamai sun koshi daga wasu yan kwangilar gwamnati, suna dira akan irin wannan Mutum suna yi masa batunci a social media, to ku ce kawai A
'UDHU BILLAHI MINAS SHAIDANIR RAJIM

" ﻣﺎ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻨﺎ ﺃﻥ ﻧﺘﻜﻠﻢ ﺑﻬﺬﺍ "

No comments

Powered by Blogger.