Giwa ta hallaka matar da ta dauke ta a hoto - Arewaweb

Giwa ta hallaka matar da ta dauke ta a hoto

< ;
Giwa ta hallaka matar da ta dauke ta hoto a Zimbabwe

Giwaye na yawan kai wa mutane hari idan suka ga ana yawan takura musu

Wani jami'in kula da namun daji ya shaida wa kamfanin dilancin labarai na AFP cewa wata giwa ta hallaka wata mata 'yar kasar Jamus mai shekara 49 a wani shahararren wurin ajiye namun daji a Zimbabwe.

Giwar ta hallaka matar bayan ta dauki garken giwaye hotuna a wani wajen shakatawa da ake kira Mana Pools a arewacin kasar, in ji Tinashe Farawo, mai magana da yawun hukumar Zimbabwe Parks da hukumar kula da namun daji.
Mr Farawo ya kara da cewa:

"Bayanan da muke da shi shi ne, 'yan yawon bude ido sun ci karo da garken giwaye a lokacin da suke shiga wurin shakatawar sai suka fara daukar hotuna.

No comments

Powered by Blogger.