2019 Zakusan Me Ake Kira Aiki Idan Na Zarce - Arewaweb

2019 Zakusan Me Ake Kira Aiki Idan Na Zarce

< ; Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Ikirari Tare da yiwan Yan  Najeriya alkawarin ganin bambanci mai yawa Idan ya zarce - A 2015, ya jawo hankalin yan Najeriya ne da alkawarin habaka tattalin arziki, kawo karshen rashawa da Boko Haram - Matsalar kasar shine manyan ta ke kwashe kudaden kasar 


Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yayi alkawarin cewa yan Najeriya zasu ga bambanci Idan suka sake zabar shi a zabe mai zuwa. A 2015, Buhari ya jawo hankalin yan Najeriya ne da alkawarin habaka lalataccen tattalin arzikin kasar, kawo karshen rashawa da cin nasarar yaki da Boko Haram. Shugaban ya hori yan Najeriya dasu sake bashi dama ta biyu domin ya cigaba da aiyukan da ya fara. Ya fadi hakan ne a jawabin da yayi wa yan Najeriya mazauna Amurka a ranar juma'a. "Zan bar mabambantan abubuwa a ofishin nan," inji shugaban kasar. Buhari ya kara da cewa, babbar matsalar Najeriya shine manyan kasar da ke kwashe kudin kasar don azurta kansu. Ya kuma tuna yanda ya garkame su lokacin da yayi shugabancin kasar a mulkin soja. 

"A 1983, sojojin kasar suka nada ni shugaban kasar. Na kwashe yan siyar duk na zuba su a kurkuku, na sanar dasu gaskiyar su kadai zata fitar dasu," inji Buhari.

Muka kwace abubuwan da suka sata, amma bayan nima an kulle ni, sai aka maida ma yan siyasan abubuwan da suka sata. Wadanne masu kudin ne sukayi korafi akan haka? " Shugaban kasar ya tuna lokacin da yake Chiyaman din PTF, yayi tituna daga Legas zuwa Abuja, zuwa Onitsha, zuwa Port Harcourt. Tun daga nan ba a kara yin su ba, "Amma masu kudin basu ce komai ba akai," "Ana kira na baba-tafiya-a-hankali, amma wadanda ke gudun ina suka kai? " 



No comments

Powered by Blogger.