Mece ce makomar Ozil da Luiz da Mignolet da Rose da kuma Mata - Arewaweb

Mece ce makomar Ozil da Luiz da Mignolet da Rose da kuma Mata

< ;

Mirror ta ruwaito cewar kocin Arsenal, Unai Emery, yana fatan karin kokari daga dan wasan tsakiya na Jamus mai shekara 29 Mesut Ozil, wanda
 bai samu shiga wasan da kulob din ya yi nasara a kan West Ham da 3-1 ba saboda rashin lafiya.

Dan wasa bayan Brazil, David Luiz, mai shekara 31, ya ce ya zame masa dole ya bar Chelsea idan Antonio Conte ya ci gaba da kasancewa kocin kungiyar, in ji Sky Sports.
Golan Liverpool Simon Mignolet, mai shekara 30, ya ce abin "mamaki ne" cewar kulob din ya kyale golan Jamus Loris Karius ya koma buga wasan aro a Besiktas . Dan kasar Belgium din ya ce bai san makomarsa ba a Anfield, kamar yadda
Liverpool Echo ta ruwaito.

Dan wasan bayan Tottenham Danny Rose, mai shekara 28, zai iya komawa Marseille -buga wasan aro ko kuma kan yarjejeniyar din-din-din -a wani yunkuri na inganta damammakinsa a Ingila, in ji Star.

Hakazalika Mirror ta ruwaito cewar Manchester United ba ta yi wani yunkurin dan wasan baya Rose ko kuma dan wasan bayan Belgium Toby Alderweireld, mai shekara 29, daga Spurs a lokacin kasuwar musayar lokacin bazara duk da cewar an alakanta su da kyau.

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya shaida wa 'yan wasansa cewar dole dukansu su sake faranta mishi rai bayan an tilasta masa sake cigaba da 'yan wasansa na da bayan gasar kofin duniya, in ji Telegraph.

Sai dai kuma, Pochettino ya ce takwaransa na
Manchester United Jose Mourinho wani abin "koyi ne" ga koci-koci matasa , in ji Sun.

Kocin Newcastle Rafael Benitez ya ce ya amince da jinkirta tattaunawa game da makomarsa zuwa shekara mai zuwa. Dan kasar Sifaniyar, wanda aka yi tsammanin cewar zai rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya a wannan kakar, ya ce yana "tunanin wasanni ne kawai," kamar yadda Goal ta ruwaito.

Dan wasan Juventus dan kasar Croatia Mario Mandzukic, mai shekara 32, ya ki tayin komawa
Manchester United , in ji Calciomercato -ta Sun.

No comments

Powered by Blogger.