Ladan Da Ake Samu Bayan An Gama Saduwa Da Iyali - Arewaweb

Ladan Da Ake Samu Bayan An Gama Saduwa Da Iyali

< ;


An ruwaito cikin littafin shifa’u sudur” cewa Annabi (SAW) yace idan mace ta shiga cikin shaanin hidimar mijinta ko tayi kwalliya domin neman yardar sa.

ALLAH (SWT) zai rubuta mata lada guda goma kuma ya daukaka mata darajarta idan mijinta ya kirata tayimasa biyayya har ta dauki ciki zata kasance tanada ladan mai yin azumi da salloli dare kullum a wajen daukaka kalmar ALLAH wato jihadi”.

A’isha(RA) tace hakika an baiwa mata alheri masu yawa to menene ku agareku maza?
Sai annabi(SAW) yayi dariya yace “Babu wani mutum da ya riki hannun matarsa da nufin yin jima’i da ita sai ALLAH(SWT) yarubuta masa kyawawn ayyuka guda biyar idan yahada wuya da ita yanada lada guda goma idan ya

sumbacceta (kiss) yanada lada guda ashirin idan ya sadu da ita ALLAH (SWT) zai bashi ladan da yafi duniya da abunda yake cikinta idan yatashi domin yin wankan (janaba) ruwan wankan bai gudanaba a wani bangaren jikinsa sai an shafe zunubansa a kuma daukaka masa darajarsa.

A na bashi ladan abinda yafi duniya harda abinda ke cikinta saboda wannan wankan da yayi kuma ALLAH (SWT) yana yima mala’ikunsa kirari yana cewa ((‘ku dubi bawanaacikin dare mai sanyi yana wankan janaba ya
sakankance nine Ubangijinsa” to ina shaida muku na gafarta masa ”)).

ALLAH KA BAMU IKON SADUWA DA MAZANMU NA SUNNA.

No comments

Powered by Blogger.