Naira dubu 900: Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano - Arewaweb

Naira dubu 900: Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano

< ;


Babban Limamin masallacin Juma'a na unguwar Tudun Murtala dake a garin Kano,


Sheikh Abdullahi Sale Pakistan ya hadu da fushin hukuma bayan da wata babbar kotun jihar ta umurci ya mayar da wasu kudaden da ya ansa na masallacin da ya karba.

Kudin dai kamar yadda muka samu sun kai adadin Naira dubu dari tara sannan kuma ya karbe su ne da sunan bashi kusan shekaru biyu kenan da suka gabata.

Mun samu cewa Alkalan babbar kotun jihar Masu Shari'a Patricia A. B. Mahmoud da kuma Abdullah Mahmoud Bayero sune suka yanke hukuncin bayan sun yi fatali da hukuncin da wata karamar kotu a jihar ta yanke akan lamarin.

Haka zalika mun samu cewa tun farko dai kudin da aka tara suna a hannun kwamitin amintattu ne na gidauniyar ida kammala ginin masallacin tunawa da Sheikh Jafar a unguwar Sabuwar Gandu da ke a karamar hukumar Kumbotso.

No comments

Powered by Blogger.