Labarin wani kare da ke zuwa masallaci Sallah sau 5 a rana a garin Zariya - Arewaweb

Labarin wani kare da ke zuwa masallaci Sallah sau 5 a rana a garin Zariya

< ;

Wani batu da ya dade yana daurewa jama'ar unguwar Tudun Wada a garin Zariya kai da ma al'ummar musulmi da dama shine labarin wani kare da ke zuwa masallaci wajen Sallah sau biyar a kullum rana tare da musulman unguwar.

Da majiyar mu ta zanta da mai karen, Jubril Mohammed, ya shaida mata cewa babu mai jan karen zuwa masallaci shine ke kai kan sa da zarar ya ji kiran sallah kuma da an kammala ya taso ya taho gida ya jira kiran sallah na gaba kuma.


Malam Jubril ya kara da bayyana cewa karen ya soma yin hakan ne kusan shekaru bity da suka gabata kuma ma yanzu har zuwa jana'iza yake yi kuma a duk inda yaje, yakan samu wuri ne kusa da jama'a ya zauna har su kammala.

 Da aka tambayi masana kimiyyar dabbobi ko me za su ce game da hakan, sun bayyana cewa daman akwai dabbobin da Allah yayi wa baiwar kwaikwayon mutane tare da dabi'antuwa da wata halayya idan har an koya masu wanda kare ma yana ciki.

No comments

Powered by Blogger.