Allah yayi: 'Yan gudun hijira fiye da 6000 sun koma gidajensu a Zamfara - Arewaweb

Allah yayi: 'Yan gudun hijira fiye da 6000 sun koma gidajensu a Zamfara

< ;


Bayan kwashe watanni suna zaune a sansanin 'yan gudun hijira, al'ummar jihar Zamfara sun fara komawa gidajensu saboda sojoji da sauran jami'an tsaro sun fara cin galaba kan 'yan bindigan da suka adabi jihar.

Mukadashin direktan yada labarai na hedkwatan tsaro, Brigadier Janar John Agim ya sanar da cewa sama da 'yan gudun hijira 6000 sun koma gidajensu a jihar Zamfara.

Agim ya bayar da wannan sanarwan ne a ranar Juma'a yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Ya ce 'yan gudun hijira da yawa a kananan hukumomin Maradu, Shinkafi da Zurmi sun baro sansanin 'yan gudun hijira sun koma gidajensu saboda an samu tsaro da kwanciyar hankali a kauyukan.

Mr Agim ya ce monama da 'yan kasuwa sun fara gudanar da sana'o'insu kamar yada suka saba saboda yanzu ba su faragaban cewa 'yan bindiga za su sake kawo musu farmaki.

Ya ce a baya 'yan bindiga, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami ne ke cin karensu babu babaka a jihar amma a yanzu ya tabbatar da cewa hukumar zata bawa mutane da dukiyoyinsu kariya.

Kazalika, Agim ya ce samamen sama da sojin Najeriya na Operation Sharan Daji suka kai a Sububu da Rugu ya yi tasiri sosai wajen karya gwiwar 'yan bindigan tare da taimakawa sojojin wajen cin galaba a kansu.

Mukadashin direktan yada labaran ya ce hukumar za ta cigaba da kara kaimi wajen kawar da masu aikata laifuka da yakan 'yan bindigar har sai an ga bayansu a jihar.

No comments

Powered by Blogger.