Tantiran tsagerun Neja Delta sun yi barazanar dagulawa Shugaba Buhari lissafi - Arewaweb

Tantiran tsagerun Neja Delta sun yi barazanar dagulawa Shugaba Buhari lissafi

< ;


- Tsagerun Neja Delta sun yi barazana ga Shugaba Buhari
- Sun ce za su cigaba da kai hare-hare
- Sun yi kaca-kaca da jam'iyyar APC

Tantiran tsagerun nan na Neja Delta a karkashin wata gamayyar kungiyoyi da suka kira Coalition Niger Delta Agitators sun yi barazanar cigaba da kai sabbin hare-hare akan bututan mai dake a yankunan su idan dai har gwamnatin Buhari bata sake fasalin kasar nan ba.

e a cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kungiyoyin Mista John Duku ya fitar dauke da sa hannun sa a ranar Asabar din da ta gabata a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

a cikin sanarwar, tsagerun sun yi Allah-wadai da irin salon mulkin jam'iyyar APC da sukace kwata-kwata yayi hannun riga da na demokradiyya tare da jan hankalin Shugaba Buhari da ya gaggauta biya masu bukatun su.


A wani labarin kuma, Yanzu haka dai harkokin tattalin arziki na cigaba da tabarbarewa yayin da baitul mali na Najeriya a babban bankin kasar watau Central Bank of Nigeria ya yi kasa da dalar Amurka miliyan 990 a cikin sati uku kacal da suka shude.


Wannan dai na kunshe ne a cikin rahoton da babban bankin ya fitar majiyar mu kuma ta Punch ta same shi a ranar Lahadin da ta gabata.

No comments

Powered by Blogger.