Shin ya dace a kwankwadi giya Kuma Hakan yanada Illa ga Lafiyar mu? - Arewaweb

Shin ya dace a kwankwadi giya Kuma Hakan yanada Illa ga Lafiyar mu?

< ;

Ga wani labari maras dadi ga mutanen da ke ganin shan giya kwalba daya a duk rana yana da alfanu.

Wani bincike da aka yi a duk fadin duniya wanda aka wallafa a mujallar Lancet ya tabbatar da binciken da aka yi a baya cewa shan giya ba shi da wani amfani ko da na sisin kwabo.

Masu binciken sun amince cewa shan giya kadan ka iya hana kamuwa da ciwon zuciya amma sun gano cewa illar da shan giya zai yi wajen haddasa cutar daji da sauran cutuka ya fi alherin da ke cikin ta.

Sun kara da cea wannan shi ne bincike mafi girma a kan shan giya zuwa yanzu domin kuwa sai da ya tabo bangarori da dama.

Wacce irin cutarwa shan giya ke yi?
Binciken da The Global Burden of Disease ta gudanar ya yi nazari kan yadda ake kwankwadar giya da kuma tasirin ta ga lafiyar jama'a a kasashe 195, ciki har da Burtaniya, tsakanin 1990 da 2016.

Da yake duba alkaluman 'yan shekara tsakanin 15 zuwa 95, binciken ya kwatanta mutanen da ba su taba shan giya ba da kuma wadanda suke sha sau daya a kwana.
Ya gano cewa a cikin mutum 100,000 da ba sa shan giya, mutum 914 ne ke fama da cutukan da ba su da alaka da shan giya irin su cutar daji.

Sai dai binciken ya gano cewa karon mutum hudu ka iya kamuwa da cutukan idan har sun taba shan giya ko da sau daya ne a rana - wato an samu karuwar kasadar kamuwa da cutukan da kashi 0.5 cikin dari.

Kazalika binciken ya gano cewa karin mutane 63 ne ke kamuwa da cutar daji da makamantan ta idan suka sha giya kwalba biyu a kullum - kasadar kamuwa da cutukan da kashi bakwai cikin dari ke nan.

Haka kuma mutanen da ke shan giya kwalba biyar a kullum, za su fuskanci kasadar kamuwa da cutar daji da kshi 37 cikin dari.

Daya daga cikin masu binciken, Farfesa Sonia Saxena, ta Jami'ar Imperial College da keLondon kuma likita ta ce: "Shan giya kwalba daya a rana ba shi da hatsari sosai, amma idan ka yi la'akari da yawan mutanen Burtaniya za ka ga hakan na da girma, kuma akasarin mutane ba sa shan kwalba daya su hakura."

No comments

Powered by Blogger.