Rikicin Kaduna: Buhari ya fusata, ya sanar da matakin da zai dauka - Arewaweb

Rikicin Kaduna: Buhari ya fusata, ya sanar da matakin da zai dauka

< ; A yau Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sanarwar saka dokar ta baci tare da hana mutane fita na tsawon sa'o'i 24 a kwaryar birnin Kaduna da kewaye domin dakile yaduwar tarzomar da ta tashi a garin.
A daren yau ne shugaba Buhari ya yi alla-wadai da rikicin na jihar Kaduna da ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane 55 tare da bayyana cewar ba zai taba yarda da wofantar da ran bil'adama da zubar da jini ba. Buhari ya ce babu wani addini da ya yarda da tashin hankali. A sakon da shugaban ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewar tilas ya yi tofin ala-tsine a kan rikicin da ya yi sanadin rasa rayuka 55. Shugaba Buhai ya bayyan cewar ya bawa rundunar 'yan sanda damar daukan dukkan matakin da zai kai ga dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Kaduna. Kazalika ya bayyana cewar ya umarci shugaban rundunar 'yan sanda ya tura runduna ta musamman tare da sanar da shi halin da ake ciki a kan lokaci.


Buhari Source: Depositphotos "Ina mai tabbatarwa da dukkan 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da karfi da ikonta domin kare kowa da kowa. Ba zan taba yarda da wofantar da rayuwar bil'adama ba. Babu wanda tashin hankali ke amfana. Ina rokon shugabannin al'umma da na addinai su rungumi sulhu, sasanto da kasancewa masu hakuri domin gudun cigaba da yaduwar rikici," a kalaman shugaba Buhari. 

Kazalika, shugaban ya jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa daukan matakin gaggawa a kan rikicin. A wata sanarwa da Samuel Aruwan, mai taimaka gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna a bangaren yada labarai, ya fitar, ya bayyana cewar dokar hana fitar za ta fara aiki nan take. Dokar ta bacin na zuwa ne kwanaki uku bayan barkewar rikici mai nasaba da addini a kasuwar Magani da ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane 55 da asarar dukiya mai tarin yawa.


No comments

Powered by Blogger.