Ankashe Mutane Tare Da Kone Motocinsu A Garin Kaduna
<
;
Bayan asarar rayukan mutane 55, gwamnati ta saka dokar hana fita a kwaryar Kaduna
A yau Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sanarwar saka dokar ta baci tare da hana mutane fita na tsawon sa'o'i 24 a kwaryar birnin Kaduna da kewaye domin dakile yaduwar tarzomar da ta tashi a garin
A wata sanarwa da Samuel Aruwan, mai taimaka gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna a bangaren yada labarai, ya fitar, ya bayyana cewar dokar hana fitar za ta fara aiki nan take.
Dokar ta bacin na zuwa ne kwanaki uku bayan barkewar rikici mai nasaba da addini a kasuwar Magani da ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane 55 da asarar dukiya mai tarin yawa.
Da ranar yau, Lahadi, ne wani sabon rikicin ya nemi ya barke a garin Kaduna bayan bullar wata jita-jita da ta saka mutane cikin firgici da gudun neman mafaka. Kazalika akwai rahotanninn da suka bayyana cewar an kone motoci a kan titin Ahmadu Bello da kuma jin karar harbin bindiga a titin Jos.
No comments