Tsohuwa yar shekara 100 ta amshi addini muslinci [ photo] a Abuja - Arewaweb

Tsohuwa yar shekara 100 ta amshi addini muslinci [ photo] a Abuja

< ; A birnin tarayya

Anyi ittifaki duk garin Karshi dake garin Abuja, babu sa'anta kuma ta amshi musulunci bayan shekaru da dama da yaran ta ke fama da ita wajen karbar addinin

Wata dattijiya mai shekaru 100 a duniya wacce aka yi ittifakin babu sa'anta a yankin Karshi dake Abuja ta karbi musulunci.
A bisa labarin da jaridar RARIYA ta fitar, bayan shafe shekaru ana fama da ita musamman 'ya'yanta da jikokin ta amman abin ya gagara, sai gashi sanadiyar Mauludin da aka shirya don auren wani jikanta daga nan Allah ya sa mata zuciyar musulunci.

Babban limamin garin Karshi, Sheikh Adamu Inuwa ya ce, "akwai lokacin da ta tara 'ya'yanta tace duk wanda ya kara cewa ta shiga musulunci sai ta yi Masa Baki, wannan yasa suke jin shakkar kiran ta zuwa musulunci, amman ni duk da haka ban gaji da zuwa wajanta ba don da'awah".
Wani abun mamaki ga ita wannan baiwar Allah duk sanda ake Mauludin Manzon Allah SAW sai ta fito, har ma tana fadin duk sanda ta ji an ambaci Manzon Allah SAW takan samu nutsuwa a zuciyar ta.

Ta amshi kalmar shahada kuma ta zabi suna Rahama a matsayin sabon sunan musulunci ta.

No comments

Powered by Blogger.