Subahanallahi! 'Yan bindiga sun kashe mutum 11 a Badarawa a jihar Zamfara - Arewaweb

Subahanallahi! 'Yan bindiga sun kashe mutum 11 a Badarawa a jihar Zamfara

< ;

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kisan mutane shida a kauyen Badarawa a yankin karamar hukumar Shinkafi a jihar.

Kakakin 'yan sandan jihar ta Zamfara, Mohammed Shehu ya fada wa BBC cewa, wasu mutum 10 kuma sun ji rauni a harin.
Ya kara da cewa jami'an 'yan sanda tare da sojoji sun shiga daji domin farautar maharan.

To sai dai bayanan da ke fitowa daga kauyen na Badarawa sun ce mutum 11 ne aka kashe yayin da 'yan bindiga sun bude wuta kan wani taron jama'a.
Bayanan sun ce galibin wadanda lamarin ya rutsa da su matasa ne.

Haka ma an ce wasu mutanen 23 sun samu raunuka lokacin da 'yan bindigar suka kai wannan harin.

Tuni dai aka yi jana'izar mutane da suka riga mu gidan gaskiya a harin na 'yan ta'adda.

Bayan jana'izar wadanda suka rasu dazu da safe, Bashir Umar Badarawa, daya daga cikin wadanda suka binne mutanen ya bayyana wa BBC cewa harin ya auku ne a daidai misalin karfe uku na daren Laraba.
"Akwai yaron da ke sana'ar sayar da shayi a kusa da masallacin 'yan izala na garin Badarawa inda wasu matasa suka taru suna kallon talabijin. To sai 'yan bindigan suka zagaye wurin kana suka bude musu wuta."
Ya bayyana cewa a sanadiyyar wannan harin mutum 11 sun mutu nan take, mutum 23 kuma sun sami raunuka.
Ya kuma ce, "Maharan su 16 ne suka kai wannan harin."


Bashir Umar ya ce babu wanda ya san dalilin da ya sa wadannan maharan suka kai harin a garin na Badarawa.
"Ka san jihar Zamfara na fuskantar wannan matsala ta rashin tsaro, domin haka bamu san dalilan da suka sa wadannan maharan suka kai wannan harin ba."

Mallam Bashir ya koka da halin da yankin ya fada a yanzu: "A halin yanzu mazauna garin Badarawa da makwabtansu na zaune cikin fargaba a dalilin wannan harin da aka kai."

"An hana mutane su dauki makaman da za su kare kansu, kuma gwamnatin nan ta kasa samar da wadataccen tsaron da zai kare rayukan mutane."

To sai dai gwamnati na cewa tana bakin kokarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar.

Ko a 'yan watannin bayannan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura sojoji da sauran jami'an tsaro 1,000 jihar ta Zamfara domin magance matsalar tsaro da ake fama da ita.

No comments

Powered by Blogger.