Babbar magana: An kama mai kula da dandalin WhatsApp da matan aure a Kano - Arewaweb

Babbar magana: An kama mai kula da dandalin WhatsApp da matan aure a Kano

< ;

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mai kula da shafin WhatsApp, wato admin, da wasu matan aure bisa zargin yada labarin karya.

Kakakin 'yan sanda na jihar, SP Magaji Musa Majiya, ya shaida wa BBC cewa mutanen suna yada hoton wata matar aure ne tare da yi mata kagen cewa tana satar yara a birnin Kano.


Majiya ya ce matar, wacce ma'aikaciyar gwamnati ce, ta kai musu korafin cewa ana yada hotonta a WhatsApp da nufin bata mata suna, da kuma yunkurin jefa rayuwarta cikin hadari.

Ya ce daga nan ne suka fara bincike, abin da ya kai su ga kama mutum uku, namiji daya da mata biyu, kuma dukkan su masu aure ne.

Kakakin na 'yan sanda ya ce mutanen sun tabbatar musu cewa su ma sun samu hoton ne, don haka suka ci gaba da yada shi.
Mutanen da aka kama dai sun shaida wa 'yan sanda cewa ba su san matar ba, kuma ba su yi yunkurin tantance labarin ba gabanin su fara yada shi, don haka suna neman gafara, kamar yadda Majiya ya shaida wa BBC.

Tuni dai rundunar 'yan sandan ta yi holin mutanen ga 'yan jarida, to amma an bayar da belin su daga baya.

Kafar sadarwar ta WhatsApp dai ta zama wata hanya da ake yada labari da hotuna da bidiyo cikin sauki, ba kuma tare da jama'a sun tantance sahihancin abin da suke yadawa ba.

Mutane da dama dai na nuna damuwa da yadda ake amfani da kafar, musamman wajen yada labaran kanzon kurege, da ake ga za su iya jefa rayuwar jama'a cikin hadari.

Kimanin mutum biliyan daya ne ke amfani da kafar sadarwar ta WhatsApp a kullum a duniya, kamar yadda kamfanin ya bayyana.
A nahiyar Afirka ma dai jama'a sun fi amfani da manhajar ta WhatsApp wajen aikewa da sakwanni.

Wasu alkaluma na nuna cewa Najeriya ce kan gaba a nahiyar wajen amfani da manhajar ta WhatsApp inda kimanin mutum miliyan 40 zuwa 60 ke amfani da manhajar a kasar.

No comments

Powered by Blogger.