Jarumin Nollywood ya bada dalilin da yasa ya saka Hadiza Gabon a cikin shirin sa - Arewaweb

Jarumin Nollywood ya bada dalilin da yasa ya saka Hadiza Gabon a cikin shirin sa

< ;

Ta shaida cewa ta amince da fitowa cikin shirin bisa ga ka’ida na cewa baza ta fito a matsayin da zai sabawa addini ko al’adar ta.

A kwanan baya mun kawo maku labarin cewa fitacciyar jarumar Kannywood ta fito a cikin wani shirin fim na turanci wanda shine na farko da zata yi aiki a masana'antar fim na Nollywood.
Jaruma mai tauraro ta nuna farin ciki game da wannan damar na yin fim da wasu jiga-jigan yan wasan Nollywood.

Ta shaida ma BBChausa cewa ta amince da fitowa cikin shirin bisa ga ka’ida na cewa baza ta fito a matsayin da zai sabawa addini ko al’adar ta.
Advertisement
Tana mai cewa;

“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna 'Lagos real fake life'
"Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al'adata ba"
Jarumar ta shaida cewa babu wani bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finai a kannywood da nollywood face bambancin harshe.

Shahararren jarumi wanda ya shirya shirin yayi karin haske game da dalilin saka jarumar cikin shirin duk da cewa bata taba fitowa a cikin wani shirin Nollywood.
Zantawa da muka yi dashi yayin da ya kawo mana ziyara, Mike Ezurounye ya nuna gamsuwar sa yin aiki da ita.

Yayin da yake bada amsar dalilin saka ta a shirin, jarumin yana mai cewa "Ni mutum ne wanda ke son saka abun mamaki a cikin fim. Hadiza tana da basira, ta kware kuma bata taba yin fim a Nollywood ba"

"Na ware lokaci na musamman domin inyi bincike akan ayukan ta kuma na tambayi jama'a da dama game da basirar ta" ya kara.

Mike yace Hadiza ta bada hadin kai dari-bisa dari kamar yadda ya kamata kuma a bangaren su sun kiyaye duk wani ka'ida da al'ada da addininta ya tanadar.
A cewar shi ya ji dadin aiki da ita matuka kuma akwai wasu aiki biyu da zai so ya kara saka ta a ciki.

Daga karshe jarumin ya jinjina ma masana'antar Kannywood, yace kofar shi a bude take wajen yin aiki da masa'antar.
Shirin 'Lagos real fake life' tana fadarkar da jama'a game da rayuwar karya da wasu suka sa a ransu. Manyan fitattun Nijeriya daga masana'antar fina-finai dake kasar suka fito a ciki har ma da jaruman kasashen waje.

Za'a fara haska ta ga sinima cikin watan Nuwamba.

No comments

Powered by Blogger.