Dan Adam Zango ya fara wakar hip-hop - Arewaweb

Dan Adam Zango ya fara wakar hip-hop

< ;

Masu ruwa da tsaki da sauran jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan aniyar da babban dan fitaccen jarumin Kannywood Adam Zango ya nuna ta zamowa mawakin hip-hop.

A makon da ya gabata ne yaron mai suna Ali Haidar Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa zai fitar da kundinsa na farko masu dauke da wakoki masu taken Godiya da Rayuwa.

Shi ma mahaifin yaron ya yi ta wallafa hotunan dan nasa yana mai nuna goyon baya tare da yi masa fatan alheri a wannan aiki da ya fara.

Haidar Zango wanda ake yi wa lakabi da "Star Boy" ya ce mahaifinsa ne ya gano basirar da yake da ita ta iya waka.
Yaron dai ya sha alwashin ba zai bai wa mahaifinsa kunya a wannan lamari ba, inda ya wallafa cewa "zan tabbatar da mahaifina ya yi alfahari da ni."

Wani makusancin Adam Zangon a fagen shirya fina-finai, Tahir I Tahir, ya shaida wa BBC cewa tuni har an nadi waka ta farko daga cikin wakokin nasa.

Tahir ya kuma ce Zango ba zai taba yin wasa da lamarin karatun dansa ba, don a yanzu haka ma yana wata makarantar Arabiya mai hade da Boko inda yake haddar Al-Kur'ani.

"A yanzu haka hutu suke yi shi ya sa mahaifinsa ya bar shi har yake harkar wakar, amma da zarar an koma makaranta zai tafi," in ji Tahir.

Wane ne Ali Haidar Zango
Yaro ne da bai gaza shekara 10 ba
Yana wata makarantar firamare ta kwana ta Farfesa Ango Abdullahi a Zariya
Kashi 80 na tsarin makarantar karatun Arabiya ne yayin da kashi 20 kuma ake Boko

Yana da haddar izu hudu daga Suratul Bakara
Yana da shafin Instagram mai mabiya kusan 28,000
Me mutane ke cewa?

Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a wasu shafukan sada zumunta bayan da wannan labari ya bayyana.
Wasu dai na ganin hanyar da yaron ya dauko ba mai bullewa ba ce har ma suka yi ta zargin mahaifin nasa da cewa kamata ya yi ya bai wa dan ingantaccen ilimi maimakon zama mawaki.

Amma a bangare guda wasu suna ganin zama mawaki ga yaro ba wani abu ba ne tun da ita kanta waka baiwa ce da ba kowa Allah ke bai wa ba.

Don haka ne ma suka yi ta jinjina wa jarumin da cewa mara wa aniyar dan nasa baya wani abu ne mai kyau kwarai.

A baya-bayan nan dai ana yawan samun bullowar yara kanana da ke zama mawakan hip-hop a arewacin Najeriya, musamman tun bayan mutuwar Lil Ameer, wani yaro da ya shahara a wakokin hip-hop.

No comments

Powered by Blogger.