Adam Zango ya nemi gafarar Ali Nuhu - Arewaweb

Adam Zango ya nemi gafarar Ali Nuhu

< ;

Shahararren jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango, ya nemi gafarar jarumi Ali Nuhu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sakon mai dauke da wani hoton da ya nuna Zango ya durkusa kuma Ali na zaune bisa kujera, ya zo ne kwanaki bayan Zangon ya wallafa wasu hotunansa da Ali a Instagram bayan sun kwashe kwanaki suna "gaba".
Sakon Adam Zangon ya ce "tuba nake sarki gwiwowina a kasa".

Tuni dai magoya bayan jarumin suka fara tofa albarkacin bakinsu kan hoton da Zangon ya wallafa a shafinsa na Instagram.


Rayuwar Adam A Zano a takaice
An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa

Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16


Rayuwar Ali Nuhu a takaice
An haife shi a watan Maris na 1974
Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya

Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki
Jaruman biyu suna gaba-gaba a masana'antar Kannywood din inda suke da mabiya da dama a shafukan sada zumunta.

No comments

Powered by Blogger.