"HAKKIN UWA" baya Karewa Akan Dan Adam Harsai ranar da ya koma ga mahaliccinsa - Arewaweb

"HAKKIN UWA" baya Karewa Akan Dan Adam Harsai ranar da ya koma ga mahaliccinsa

< ;

Wani yaro ne ya zauna yana tadi da mahaifiyarsa sai yake nuna mata yadda yake son ta da kaunar ta, ita ma tana fada ma sa yadda take matukar son sa. Daga cikin abin da take gaya masa ta ce, na sha wahala kwarai wajen rainon cikin ka.


Allah ne kawai ya nufi zan rayu. Ga shi kuma ka tashi mai yawan ciwo a kullum ina kan hanyar asibiti.


Da dare kuma ba na samun bacci saboda yawan kukanka. A cikin raha sai ta ce masa, yanzu idan ka girma da me za ka saka min ne? Ya ce, Mama kada ki damu, idan na girma zan samu aiki mai kyau da albashi mai kwari sai in rika sawo maki duk abin da kike so.


Ta ce, ai wannan daman mahaifinka yana yi. Kuma ka ga ma kafin ka girma tsufa ya fara kama ni, ba ni bukatar jin dadi fiye da wanda nake ji a yanzu. Ya ce, to Mama ba wata damuwa, zan auro Mata mai hankali da kirki wacce za ta rika girka maki abinci, ta share dakinki, takula da ke sosai.

Ta ce, a’a. Wannan ai ba aikinta ba ne. Kuma ba za ka aure ta don wannan ba, don Allah bai dora mata yin haka ba. Ni ma kuma ba haka nake bukata wurin ta ba. Za ka auri Mace ne don bukatar kanka da kula da ‘ya’yanka idan Allah ya ba ku. A nan ne fa ya yi shiru, ya nunfasa, sannan ya ce, Umma! To me zan yi in biya ki kenan? Ta ce, alhamdu lillahi. Ka zo ga tambayar da nake so ka yi min.

Kada ka bar ni. A kowane hali da kuma duk in da kake ka rika bin labarina; ka ziyarce ni ko ka buga min waya, ka rika debe mini kewa da jin duriyarka. Idan ajalina ya zo ka runguma ni tare da jama’a ku kai ni makwancina. In kun rufe ni ka tsaya ka yi mani addu’a. Sannan ka yawaita yin sadaka a gare ni. A duk sallah ka rika sa ni cikin sujudarka kana neman rahamar Allah a gare ni.


Ka tuna cewa, duk aikin alheri da kake yi ina da kamasho a cikin sa. Sannan ka sani cewa, daukar cikinka da na yi da rainon ka ba aiki ne da na yi shi bisa wata yarjejeniya ba.

Samun ka wata baiwar Allah ce da kyautarsa da ya sanyaya rayuwata da ita. Tare da haka kuma yana ba ni dinbin lada a kan ta. A nan ne fa yaron ya sunkuyar da kansa yana hawaye. Uwar ta rungume shi tana share hawayensa tare da yi masa addu’oi na samun nasara da ci gaba da samun dace a rayuwarsa.

*Darussa:*
- Uwa uwa ce, wacce babu irin ta.
- Ba mu iya biyan iyayenmu alhakin haifuwarsu amma muna iya saka masu ta hanyar zama na kirki da bin kyakkyawar tarbiyar da suke dora mu a kan ta.

- Muna auren mata ne don bukatar kanmu ba don su yi hidimar iyayenmu ba. Amma fa dole ne su mutunta su tare da kyautatawa a gare su. Maso uwa ya so danta. Mai son miji dole ne ta so surukarta.

- Hakkin iyaye ba ya karewa har mutuwarsu. Addu’a da yi masu sadaka da kyautata namu ayyuka duk suna cikin kyautatawa a gare su.
        Allah ne mafi sani

No comments

Powered by Blogger.