NASIHA: Mafi muhimmanci ga Kowanne Dan Adam,
<
;
Sana'arka arzikinka. Annabi Dawuda makeri ne. Annabi Zakariyya Kafinta ne. Annabi Idris madunki ne Annabinmu makiyayi ne. Nemi na kanka, zaman banza babbar cuta ce. Arziki kuma zomo ne. Zomo ba ya kamuwa daga kwance!.
Yi murmushi idan ka ga mai son ka, zai ji dadi. Yi murmushi idan ka ga mai kin ka, zai ji tsoro. Yi murmushi idan ka ga wanda ya bar ka, zai yi da-na-sani. Yi murmushi ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Murmushi karfi ne ga namiji, kwarjini ne ga fuskar macce.
Makaho idan idonsa ya bude karya sandarsa yake yi. Haka dan Adam yake da saurin manta alheri da kin tuna baya. Duk wanda za ka taimake shi yi ma sa don Allah. Idan kana jiran godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki.
Wawa shi ke fadin abin da zai aikata, mai kuri shi ke bayyana abinda ya aikata. mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa.
Gishiri da Sugar kalarsu daya ce. Banbancinsu yana bayyana ne idan aka dandana. Haka mutane su ke, sai an gwada akan san na kwarai.
Zama da mutanen kirki yana karar da kai ababe guda shida: Son Allah, da bin Allah, da ambaton Allah, da gudun duniya, da son lahira da barin girman kai.
Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su. Akwai kuma ma su kin ka duk yadda ka kyautata ma su. Kowa da kiwon da ya karbe shi.
Idan namiji bai ji dadin aure ba zai yi tunanin kara mata don ya samu jin dadi. Idan kuma ya ji dadi zai yi tunanin karawa don ya kara jin dadi. Mata ku yi hakuri karin aure dabi'a ce a cikin mazajenku.
Marar gaskiya kamar mai yagaggen wando ne duk inda zai zauna sai ya rinka kame-kame. Mai gaskiya a natse yake zamansa.
Ana gane mumini ne a wurare uku: Idan ya samu ya gode ma Allah, idan ya rasa ya koka ma Allah, idan ya shiga damuwa ya koma ma Allah
Cikakkiyar nutsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifukansa ya hanashi hangen laifin wani.
Kaifin Hankali ya tabbata ga mutumin da yayi aiki da ilimin da ya sani, komai Qankantarsa, kuma ya sanya tsoron Allah adukkan lamuransa.
Murna da annashuwa sun tabbata ga Mutumin da Tunanin hisabi ya hanashi tara dukiya ta hanyar Haramun.
Wadatar zuciya ta tabbata ga mutumin da kullum yake gode ma Allah akan kowacce baiwar da yayi masa komai kankantarta, kuma ba ya kaiwa Qarar Ubangiji awajen halittunsa.
Cikar buri ya tabbata ga Mutumin da kwadayin gamuwarsa da Allah a Lahira ya hanashi dogon burin Zaman duniya.
'Dandanon zakin imani ya tabbata ga mutumin da ya fifita Son Allah da Manzonsa akan komai na duniya da lahira.
Lada mai yawa ya tabbata ga Mutumin da yaji kalmar gaskiya (kamar irin wannan) kuma ya isar da ita izuwa zukatan al'ummah ba tare da jirkita komai acikinsa ba.

No comments