'Pogba na son koma'Pogba na son koma wa Barcelona, Madrid na son Alonso' - Arewaweb

'Pogba na son koma'Pogba na son koma wa Barcelona, Madrid na son Alonso'

< ;

Real Madrid tana zawarcin dan wasan bayan Chelsea dan kasar Spain Marcos Alonso, mai shekara 27, bayan ta sha kaye a hannun abokiyar hamayyarta Atletico Madrid a wasan Super Cup, kamar yadda jaridar (Star) ta ruwaito.

Mataimakin shugaban Real Betis, Lorenzo Serra Ferrer, ya ce kungiyar ta Seville za ta so ta sayi dan wasan gaban Tottenham dan kasar Brazil, Lucas Moura, mai shekara 26, kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, a cewar (El Desmarque - in Spanish) .

Ita kuwa jaridar (Mail ) cewa ta yi dan wasan tsakiyar Manchester United wanda ya lashe kofin duniya Paul Pogba yana son barin Old Trafford domin koma wa Barcelona.

Mourinho ya shaida wa Pogba cewa ya nemi tafiya idan yana son barin kulob din.
Dan wasan Faransan, mai shekara 25, ya mayar da martani cewa shi zai yi magana da kocin dan kasar Portugal ta bakin ejen dinsa, kamar yadda jaridar (Sun) ta ruwaito.

Har ila yau jaridar (Mirror ) ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Manchester City din mai shekara 27 Kevin de Bruyne zai yi jinyar wata uku bayan ya ji rauni a gwiwarsa ta dama.

Hakazalika jaridar (Mirror ) ta ruwaito cewa Bayern Munich tana son sayen dan wasan Tottenham,
mai shekara 29, Toby Alderweireld.
Golan Arsenal, mai shekara 29, dan kasar Colombia David Ospina ya koma buga wasan aro a kungiyar Napoli, in ji (Guardian) .

Mediaset ta ruwato cewar Parma ta kusa sayen dan kasar Ivory Coast Gervinho, mai shekara 31, daga kungiyar kwallon kafa ta kasar China Hebei Fortune.
Liverpool ta ki tayin da Torino ta yi wa dan wasan tsakiyar Serbiya, mai shkeara 22, Marko Grujic.

Kulob din na Italiya ya so dan wasan ya buga masa wasan aro ne tsawon kaka daya da zabin sayensa kan kudi fan miliyan tara a kaka mai zuwa, in ji (Liverpool Echo) . wa Barcelona, Madrid na son Alonso'

Real Madrid tana zawarcin dan wasan bayan Chelsea dan kasar Spain Marcos Alonso, mai shekara 27, bayan ta sha kaye a hannun abokiyar hamayyarta Atletico Madrid a wasan Super Cup, kamar yadda jaridar (Star) ta ruwaito.

Mataimakin shugaban Real Betis, Lorenzo Serra Ferrer, ya ce kungiyar ta Seville za ta so ta sayi dan wasan gaban Tottenham dan kasar Brazil, Lucas Moura, mai shekara 26, kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, a cewar (El Desmarque - in Spanish) .

Ita kuwa jaridar (Mail ) cewa ta yi dan wasan tsakiyar Manchester United wanda ya lashe kofin duniya Paul Pogba yana son barin Old Trafford domin koma wa Barcelona.

Mourinho ya shaida wa Pogba cewa ya nemi tafiya idan yana son barin kulob din.
Dan wasan Faransan, mai shekara 25, ya mayar da martani cewa shi zai yi magana da kocin dan kasar Portugal ta bakin ejen dinsa, kamar yadda jaridar (Sun) ta ruwaito.

Har ila yau jaridar (Mirror ) ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Manchester City din mai shekara 27 Kevin de Bruyne zai yi jinyar wata uku bayan ya ji rauni a gwiwarsa ta dama.

Hakazalika jaridar (Mirror ) ta ruwaito cewa Bayern Munich tana son sayen dan wasan Tottenham,
mai shekara 29, Toby Alderweireld.
Golan Arsenal, mai shekara 29, dan kasar Colombia David Ospina ya koma buga wasan aro a kungiyar Napoli, in ji (Guardian) .

Mediaset ta ruwato cewar Parma ta kusa sayen dan kasar Ivory Coast Gervinho, mai shekara 31, daga kungiyar kwallon kafa ta kasar China Hebei Fortune.
Liverpool ta ki tayin da Torino ta yi wa dan wasan tsakiyar Serbiya, mai shkeara 22, Marko Grujic.

Kulob din na Italiya ya so dan wasan ya buga masa wasan aro ne tsawon kaka daya da zabin sayensa kan kudi fan miliyan tara a kaka mai zuwa, in ji (Liverpool Echo) .

No comments

Powered by Blogger.