An bayyana abinda Buhari zaije yi, a yayin ziyarar da zai kai kasar China - Arewaweb

An bayyana abinda Buhari zaije yi, a yayin ziyarar da zai kai kasar China

< ;


A yau juma’a 31 ga watan Agusta ne ake shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki na kwanaki biyu zuwa kasar China, sai dai yan Najeriya da dama basu san dalilin ziyarar da Buhari zai kai ba, kamar yadda wasu ke ganin yawon hutu kawai za shi.


shugaba Buhari zai kai wannan ziyarar ne don halartar taron majalisar koli na bakwai na hadin kan kasashen nahiyar Afirka da kasar China, FOCAC da zai gudana a babban brinin Beijing daga ranakun 3 zuwa 4 ga watan Satumba.

Hadimin shugaban kasa Buhari ta bangaren watsa labaru, Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Buhariz ai fara ganawa ne da yan Najeriya mazauna kasar China, ganawar da zata gudana a ofishin jakadancin Najeriya.

Sa’annan a matsayinsa na shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, Buhari zai gabatar da jawabi a yayin wani taro tsakanin shuwagabannin kasashen Afirka da kasar China, yan kasuwa da masu kirkire kirkire yan Afirka.

Daga nan kuma sai Buhari tare da shugaban kasar China Xi JinPing da sauran shuwagabannin kasashen Afirka zasu bude taron FOCAC na shekarar 2018, mai taken ‘Hanyar kulla karfaffan dangantaka tsakanin China da Afirka.’

Bayan bude wannan taro, shugaba Buhari zai gana da shugaban kasar China Xi Jin Ping da Firaiministan kasar Li Keqiang, inda zasu tattauna batutuwan da suka shafi hanyar samar da kudaden da za’a aiwatar da wasu manyan ayyuka a Najeriya, tare da tattaunawa akan hanyar kara dankon zumunci tsakaninsu.

Daga karshe Buhari zai yi amfanin da wannan damar ta haduwarsa da shugaba Xi Jin Ping don samun bayanai daga jami’an gwamnatin China game da matsayin ayyukan da suke yi a Najeriya, musamman aikin wutar lantarki da na titunan jirgin kasa.

Daga cikin wadanda zasu raka Buhari akwai uwargidarsa Aisha Buhari, Gwamna Mohammed Abubakar, Akinwumi Ambode, Mohammed Badaru, da Rochas Okorocha, sai kuma Sanatoci da suka hada da Abdullahi Adamu, George Akume, Godswill Akpabio, Aliyu Wammako, da Minisotoci guda 9.

No comments

Powered by Blogger.