Abin mamaki. Jami’an yan sanda sun damke budurwa mai kwacen Babura - Arewaweb

Abin mamaki. Jami’an yan sanda sun damke budurwa mai kwacen Babura

< ;


- An damke budurwa mai sace baburan mutane
- Tana baiwa yan babur alewa mai kwaya domin su fita daga hayacinsu

- Daga nan sai wasu su fito dauke baburan
Hukumar yan sandan jihar Katsina sun cika hannu da wata budurwa mai suna, Zinatu Abubakar, wacce ke satan baburan yan babur bayan basu alewa mai bugarwa.

Wani jawabo da kakakin hukumar, Gambo Isa, ya saki ga manema labarai ranan Labarai a Katsina ya ce budurwar mambar wani kungiya a jihar.

Kakakin yan sandan ya ce Gide Wada ya ajiye babur din sa da ya fara ganin jiri bayan ya sha alewan da ta bashi yayinda suka nufi inda yake kaita.

Game da cewarsa, bayan ya fita daga hayacinsa da abokan aikinta; wani mai suna Abubakar da Chairman sukayi kokarin dauke babur dinsa.

Isa ya bayyana cewa ta baiwa wani dan babur, Gide Wada, wanda ya dauketa daga Kofar-Kaura zuwa Sokoto Rima a cikin garin Katsina.

Ya kara da cewa barayin suka gudu cikin dajin lokacin da mutanen anguwa suka damke Zinatu kuma suka mikawa jami’an yan sanda.

Kakakin yan sanda ya bayyana cewa Zinatu ta laburta yadda take aikata irin wadannan abubuwan a jihar Kaduna da Kano. Ya baiwa sauran yan Babur shawaran cewa kada su amshi abinci daga hannun fasinjoji.

No comments

Powered by Blogger.