Rikici tsakanin Rarara da Nazir Ahmad ya bayyana a fili karara - Arewaweb

Rikici tsakanin Rarara da Nazir Ahmad ya bayyana a fili karara

< ;

Duk irin mukamin da Buhari zai baiwa Rarara ba zai tara abinda na tara ba – Inji Nazir Ahmad

Zo mu zauna, zo mu saba, wani karin magana na Malam Bahaushe, kuma dama ai ko a tsakanin harce da hakori ana samun sabani, don kuwa anan ma wata sabuwatr bahallatsa ne ya barke a tsakanin wasu fitattun mawakan Kannywood.

Jarida Rariya ya ruwaito shahararren mawakinnan da ake yi ma lakabi da Sarkin waka, wato Nazir Ahmad yana mayar da martani ga labarin da ake yadawa na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mashahurin mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara mukamin shugaban mawakan Buhari na yakin neman zaben 2019.

magoya baya na rade radin wai Naziru na hassada da wannan cigaba da Rarara ya samu, da wannan ne Nazirun yace ko da Rarara zai kwashe shekaru dari akan wannan mukami da Buhari nada shi ba zai taba tara abinda ya mallaka ba.


A satin data gabata ne fadar shugaban kasa ta fitar da wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya dake bayyana an nada Rarara daraktan wakokin yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben 2019.

Sanarwar ta kara da bayyana sunayen mutanen dake cikin wannan kwamiti da zasu yi aiki tare da Rarara da suka hada da fitaccen dan fim din Turanci na Najeriya kuma dan majalisa a majalisar dokokin jihar legas Desmond Elliot a matsayin Kaakaki, sai kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Imo, Uche Uwgumba Nwosu a matsayin sakatare.

No comments

Powered by Blogger.