Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin - Arewaweb

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin

< ;
 tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar, saboda batun karin albashin ma'aikata.

A safiyar yau Alhamis din nan kungiyoyin kwadagon suka fara yajin aikin a fadin kasar.

Wannan ya biyo bayan tashi baran-baran a tattaunawar da suka kai daren jiya suna yi da gwamnatin Tarayyar Najeriya akan batun sabon albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar.

Kungiyoyin da suka hada da NLC da ULC da TUC sun dauki wannan matakin ne saboda abinda suka kira gazawar gwamnati wajen sauraron kokensu.

Kwamred Nasir Kabiru shi ne Sakataren tsare-tsaren hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa wato ULC a Najeriya, kuma ya bayyana wa BBC abinda ya sa suka kasa cimma matsaya tsakaninsu da gwamnati:
"Ba mu cimma daidaito ba, saboda mun dauki kiran da ministan kwadago yayi mana a matsayin yaudara ce."

Ya kuma ce, "Wannan yaji da muka tsunduma cikinsa, za mu cigaba a shi ne daga karfe goma sha biyun daren Laraba har sai illa ma sha Allah."

Ya ce da alama gwamnatin kasar ba ta damu da halin da talakan kasar ke ciki ba.
"Wa'adin da muka ba gwamnati na kwana 14 na a tattauna batun ya zo ya wuce, amma me yasa bai tashi nemanmu ba sai ana gobe za a fara yajin aiki?"

No comments

Powered by Blogger.