Kemi Adeosun na iya zuwa kurkuku na shekaru 14 sakamakon amfani da takardar NYSC ta bogi - Arewaweb

Kemi Adeosun na iya zuwa kurkuku na shekaru 14 sakamakon amfani da takardar NYSC ta bogi

< ;
- Wani lauya ya ce Kemi Adeosun ta aikata laifuka 5 da za su sanya a turata kurkuku na tsawon shekaru 14 bisa laifin mallakar takardar NYSC ta bogi
- A ranar juma'a Adeosun ta rubutawa shugaban kasa Buhari takardar murabus dinta, inda ta bayyana masa yadda aka yi har ta mallaki takardar

- Sai dai Mr. Sule ya ce wannan ajiye aikin da ta yi bai kamata ya zama karshen maganar ba, ya ce akwai bukatar a hukunta ta bisa aikata laifuka har biyar
Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria, Kemi Adeosun, wacce ta yi murabus daga wannan matsayi nata a ranar Juma'a, bisa zarginta da mallakar takardar shaidar yin bautar kasa NYSC ta bogi, na iya tsintar kanta a gidan kaso na tsawon shekaru 14.
Wani lauya, Shuaibu sule, ya lissafa laifuka biyar da ministar ta aikata sakamakon mallakar takardar NYS ta bogi.

Laifukan sun hada da buga takardar jabu, kutse ba bisa ka'ida ba, maganganunnkarya, bada bayan karya da kuma kin yin bautar kasa da ta zamarwa yan Nigeria dole ma damar sun kammala manyan makarantu, idan kuma ba su haura shekaru 30 ba.


Wadannan laifukan, na tafiya da hukuncin zuwa gidan kaso na tsawon shekaru 14, bisa dokar aikata laifuka da hukuncinsu da kuma dokar hukumar NYSC.

Badakala kan zargin Mrs Adeosun ta mallaki takardar NYSC ta bogi, ta fara bayyana ne a shafin jaridar Premium Times a ranar 7 ga watan Yuli, rahoton da ya bayyana yadda ministar ta ki yin bautar kasa amma ta mallaki takardar bogi don shaidar ta yi bautar kasan.
A ranar juma'a, fadar shugaban kasa ta sanar da murabus din Adeosun daga mukaminta, kuma ta fitar da wasikar da ta aikawa shugaban kasa, inda a ciki ta bayyana cewa ta aika laifin.
Ta ce ta samu taimako daga wasu mutane da bata bayyana sunansu ba wajen mallakar wannan takarda ta shaidar yin NYSC.

Sai dai Mr. Sule ya ce wannan ajiye aikin da ta yi bai kamata ya zama karshen maganar ba, ya ce akwai bukatar a hukunta ta bisa aikata laifuka har biyar.
Lauyan ya ce za a iya yiwa Adeosun hukunci bisa aikata laifukan da suka ci karo da sashe na 140 na dokar aikata laifuka da hukuncin su, wanda ya hada da bada bayanan karya, da ke da hukuncin shekara daya ko cin tara.
Kemi Adeosun

Ya ce laifukanta sun kuma ci karo da sashe na 364 da na 358, wanda hukuncinsu zai kai shekaru 14 a gidan kurkuku, na buga takardar jabu da kuma mallakar takardar. Haka zalika Mr Sule ya ce laifukan nata na da alaka da sashe na 366 na dokar aikata laifuka da hukuncin shekaru 14 a gidan kurkuku ko tara.

Dokar hukumar NYSC ta samar da hukuncin shekara daya a gidan kurkuku ko tarar 2,000 ga wanda ya tsallake bautar kasar, ko kuma shekaru 3 a gidan kurkuku ga wanda ya karya wannan doka.
Akwai hukuncin shekaru 3 ga wanda ya mallaki takardar shaidar NYSC ta bogi ko ya bada bayanin karya akan mallakar takardar.

Lauyan ya ce ya zama wajibi a hukunta Adeosun, don zama darasi ga wadanda ke da niyyar aikata laifi irin nata, yana mai cewa barin ta haka kawai zai zama cin fuska ga dokokin kasar.

No comments

Powered by Blogger.