Jiya ba yau ba Kalli tsofaffin hotunan Hadiza Gabon sanda take kuruciya
<
;
Idan akwai wadanda ke neman ganin tsofaffin hotunan jaruma Hadiza Gabon, toh lalle abun nema ya samu.

Ashe tun tana yar budurwa ta zama adon gani, tauraruwar bata wasa indai akwai batun abinci a cikin lissafi kuma daga ganin daya daga cikin hotunan za'a gan inda take gindin wuta tana dafa abinci.
Hadiza Gabon ta wallafa hotunan a shafin na kafafen sada zumunta inda ta masoyan ta batun muhawara.
Hoton farko an ganta inda ta ci ado har tayi hoton gayu sanda take yar budurwa.
Hoto na biyu an gan inda take girka abinci tare da wasu abokan wasan ta.
Hadiza Gabon ta fito a cikin shirin Nollywood
Zata fito cikin sabon shirin fim wanda fitaccen dan wasan Nollywood Mike Ezuronye zai shirya mai suna 'Lagos fake life'.
Wannan shine karo a farko da jarumar zata fito cikin shirin Nollywood amma ba shirin farko bane wanda take turanci a ciki.
"Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a wani gajeren fim na turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood” inji Hadiza.
Jaruma mai tauraro ta nuna farin ciki game da wannan damar na yin fim da wasu jiga-jigan yan wasan Nollywood.
Ta shaida ma BBChausa cewa ta amince da fitowa cikin shirin bisa ga ka’ida na cewa baza ta fito a matsayin da zai sabawa addini ko al’adar ta.
Tana mai cewa;“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna 'Lagos real fake life'
"Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al'adata ba"
Jarumar ta shaida cewa babu wani bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finai a kannywood da nollywood face bambancin harshe.

No comments