Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan - Arewaweb

Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan

< ; Idan ba ku manta ba a baya mun kawo maku jerin sanannun mutanen da su ka fi kowa yawan a Duniya. Wannan karo kuma mun shiga fannin ‘Yan mata ne inda mu ka kawo maku wadanda su ka fi kowa kyau a Najeriya.

Ga dai wadanda ake tunanin cewa babu kamar su duk fadin kasar:


1. Genevieve Nnaji

Da dama an yi ittifaki babu wanda ta kai Genevive kyau a Najeriya. An haifi shararriyar ‘Yar wasan kwaikwayon ne a Garin Mbiase a cikin Jihar Imo


 2. Agbani Darego

Agbai Darego wata ‘Yar kwalisa ce asalin ‘Yar Jihar Ribas. Ta taba karbar lambar yabo a matsayin wanda ta fi kowa kyau a Najeriya har ma da Afrika a 2001. Darego tana cikin kyawawan matan Duniya.

3. Oluchi Onwaegba


Ana sa Oluchi Onwaegba wanda ta fito daga Kudancin Najeriya cikin kyawawan da ake ji da su a Najeriya. An haifi Oluchi ne a 1980 kuma ta shahara wajen harkar kwalliya da kele-kele.

Bayan wadannan dai akwai irin su Slyvia Nduka wanda ta shahara a Duniya da kuma Adaora Akubilo wata Budurwa ‘Yar asalin Najeriya da ke Amurka.

No comments

Powered by Blogger.