Yanzu Yanzu: Saraki ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa - Arewaweb

Yanzu Yanzu: Saraki ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa

< ;


- Bukola Saraki ya bayyana aniyarsa na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Yace zai yi taakarar ne akarkashin lemar jam'iyyar PDP
- Shugaban majalisar dattawan ya sha alwashin kawo ci gaban Najeriya da yan Najeriya

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Ya kaddamar da kudirin nasa ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta yayinda yake zantawa da matasa masu neman takara a babban birnin tarayya, Abuja.

An tattaro inda Saraki ke cewa: “Don haka ina sanar da kudirina na takarar kujerar shugaban kasar tarayyar Najeriya a zabe mai zuwa a 2019 a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

“Nayi hakan ne tare da yakinin cewa ina da abunda ake bukata wajen kawo ci gaban Najeriya da yan Najeriya.”

 Kungiyar matasan Arewa mai suna Northern Youths for Peace and Security (NYPS), a jiya Laraba, 29 ga watan Agusta sun tsayar da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a matsayin zabinsu na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar, Salisu Magaji, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, bayan wani ganawa tare da manyan matasan arewa.

Magaji ya bayyana cewa shawarar da kungiyar ta yanke ya kasance akan yadda da tayi da cewa gwamnati mai ci ta gaza sosai sannan kuma cewa Saraki ne mutum da ake ganin yana da abunda ake bukata don ceto

No comments

Powered by Blogger.