Yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a fadar shugaba Muhammadu Buhari - Wani dan takara
<
;
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa dake a arewacin Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), watau Alhaji Sule Lamido ya ce yaki da cin hanci da rashawar da Buhari yake yi babu gaskiya a cikin sa.
Alhaji Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a garin Lokoja babban birnin jihar Kogi a cigaba da zagayawa rangadin gaisuwa da musabaha da yakeyi da jiga-jigan jam'iyyar PDP game da zaben sa.
Sule Lamido yace ko kadan babu gaskiya a cikin yaki da rashawar da gwamnatin keyi domin kuwa har a fadar shugaban kasar ma cin hanci yayi katutu sannan kuma ga tsabar yunwa an kakabawa jama'ar kasa.
A wani labarin kuma, Sanatocin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a majalisar dattawan Najeriya sun maye gurbin Sanata Akpabio da ya sauya shiga zuwa APC da Sanata Biodun Olujimi daga jihar Ekiti a matsayin shugaban marasa rinjaye.
Ita dai Sanata Biodun Olujimi ta tabayin mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti sannan kuma kafin samun sabon mukamin nata itace mataimakiyar mai tsawatarwa a zauren na majalisar dattawa.

No comments