Man U ba ta son sayar da Pogba, Lukaku zai daina buga wa Beligium - Arewaweb

Man U ba ta son sayar da Pogba, Lukaku zai daina buga wa Beligium

< ;



Manchester United ta ce ba za ta sayar da dan wasan tsakiyarta dan Faransa, Paul Pogba, wanda yake son komawa Barcelona, in ji jaridar (Sun) .

Ita kuwajaridar Mirror ta ce Arsenal tana da kwarin gwiwar ci gaba da rike dan wasa tsakiyar Wales, Aaron Ramsey, mai shekara 27, duk da cewa
Barcelona da Lazio suna son dan wasan.

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya shaida wa (Sky Sports) cewa yana ganin wasu 'yan wasan za su bar kulob din kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa duk da cewa Spurs ba ta sayi ko dan wasa daya ba a wannan lokacin bazarar.

Amma kuma (Talksport ) ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Tottenham, dan Faransa, Moussa Sissoko, mai shekara 29, ya shaida wa magoya bayan kulob din cewa shi zai tsaya a kungiyar.

Pochettino ya kuma ce yana shirin kasancewa da
Tottenham na tsawon lokaci bayan ya samu damar koma wa Real Madrid , ko Chelsea a kakar da ta gabata, kamar yadda jaridar (Mirror) ta ruwaito.

Chelsea ta tattauna da dan wasan gaban kungiyar Lyon, Nabil Fekir, mai shekara 25, a lokacin bazara, amma a lokacin bazara ta ki sayen dan kasar, Faransan, a cewar (Goal) .

Ita kuma jaridar (Sun ) ta ambato kocin West Ham, Manuel Pellegrini, yana cewa kungiyarsa ba za ta sayi dan wasan tsakiyar Ivory Coast, Yaya Toure, mai shekara 35, wanda ya kasance ba shi da kulob, tun bayan da ya bar Manchester City .

Dan wasan gaban Manchester United dan kasar Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 25, ya ce yana son ya daina buga wa kasarsa kwallon bayan kammala gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta Euro, wadda za a yi a shekarar 2020, in ji
(Business Insider) .

Real Madrid ba ta ji dadin cewa Inter Milan ta tuntubi dan wasanta na tsakiya dan kasar Croatia, mai shekara 32, Luka Modric, ba tare da fara tuntubar kulob dinsa ba, a cewar (Mundo Deportivo) .

No comments

Powered by Blogger.