Abin da addini yace ayi Ranar babbar sallah a Musulunci - Arewaweb

Abin da addini yace ayi Ranar babbar sallah a Musulunci

< ;

Masana harkar addinin Musulunci sun bayyana abin da ya dace ayi a Ranar sallar layya. Yanzu dai Musulman Duniya za su yi babbar sallah a Ranar Talata bayan an yi hawan Arafa a Ranar Litinin.

Layya na cikin manyan sunnonin na Ranar babbar sallah
Ga dai abubuwan da aka so mai zuwa idi yayi a wannan rana ta musamman

1. Wanka da kwalliya
An so mai zuwa sallar idi yayi wankan tsarki sannan kuma ya caba kwalliya na kure-adaka da safe kafin ya tafi masallaci. Sai dai duk da ana son a caba ado, ba a son ayi shigar alfahari.

2. Kame-baki
Manzon Allah SAW yayi koyi da jama’a su kame-bakin su da safiyar idi har sai an dawo daga masallaci. An kuma so wanda yayi layya ya fara lasawa da namar abin da yayi layya da ita.


3. Kabarbari
Daga cikin manyan sunnoni na wannan rana shi ne a rika yin kabbara ana kiran sunan Allah. Ga dai abin da ake fada: Allaahu akbar, Allaahu akbar, laa ilaaha ill-Allaah, wa Allaahu akbar, Allaah akbar, wa Lillaah il-hamd.

4. Taya juna murna
Haka kuma yana daga cikin koyarwar addinin Musulunci, a rika gaisawa da juna, ana taya juna murna. Ana yin addu’ar ne domin neman Allah ya karbi wannan ibada da aka yi.

5. Sauya sawun sallar idi
Ya na kuma daga cikin abin da ake so a wannan rana watau Musulmai su canza hanyar da su ka bi wajen zuwa Masallaci a lokacin da za su koma gida. Wannan ya zo a Hadisan Annabi SAW.

No comments

Powered by Blogger.